Gwamnatin Kano ta shirya bikin yaye yan Daba sama da 500 da suka tuba su ka ajiye makamansu

Gwamnatin Jihar Kano ta yi bikin yaye wasu matasa da suka shiga aikin Daba su sama da 500 a Kano.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya jagoranci bikin a madadin gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf.

An gudanar da bikin ne a dakin taro na ma’aikatar Sufuri ta jihar Kano dake kan titin Gauron Dutse

Kwamishinan yace gwamna Yusuf ne ya sahale a rika gudanar da wannan shiri na tabbatar da cewa matasa sun rungumi zaman lafiya a jihar Kano wato Tudun Mun Tsira (safe corridor project)

Da yake bayyana asalin samar da wannan tunanin, Waiya wanda shine babban jami’in gudanarwa na kwamatin samar da zaman lafiya a jihar Kano, yace tsohon kwamishinan yan sanda na Kano CP Husaini Gumel ne ya samar da shi tun lokacin yana Kwamishina a Kano.

Daruruwan matasan da ake gani a yanzu, rukuni rukuni ne da shugabannin yan Daba da suka tuba, kuma kowanne a cikinku yana da mabiya a karkashinsa, Kwamishinan yace hakan ba karamar nasara ba ce a jihar, ya yabawa matasan saboda yadda suka yadda suka rungumar zaman Lafiya.

Daga nan kwamishinan ya roki yan Dabar da su rike tubansu da kyau tsakaninsu da Allah sannan su zamo mutanan kirki.

Shima a nasa jawabin kwamishinan yan sanda CP Ibrahim Adamu Bakori yace kasancewar Kano ce ke Jagorantar  jihohin Najeriya sumamman arewacin bai kamata a rika rikice rikicen Daba da kwacen waya ba.

Ya kara da cewar bayan zuwansa Kano ya fahimci cewa ana shan kwayoyi da ayyukan Daba, wannan ta sa ya samu gwamna Yusuf domin tabbatar da samar da shirin rungumar zaman lafiya a Kano.

Cp Bakori ya kuma yabawa Gwamnan Abba wajen yafewa wadannan matasan laifukansu ganin yadda suka yadda a zauna lafiya a Kano, kuma ya nemi da ayi kokarin karasa tantancesu a basu abin yi din da aka yi musu alkawari.

Kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na Kano shima ya tabbatar da cewar hukumar sa zata bada magungunan wanke ƙwaƙwalwa ga  matasan da suka tuba dan warkewa daga abinda suka samu kansu a ciki a baya.

A nasa bangaren Dattijo Alh Gidado Mukhtar ya bayyana mutukar jin dadinsa ganin yadda wadannan zaratan matasan suka shirya karbar zaman lafiya a Kano, kuma yayi musu nasiha mai ratsa zuciya ta tsakanin uba da ya’yansa.

Sauran mahalarta taron sun haɗar da sarkin shanun Kano,Alhaji Shehu Muhammad Dankadai.

Mataimakin Shugaban jami’ar Northwest Farfesa Muktar Atiku Kurawa

Shugaban kwamitin Tsaro na jihar Kano
Alh Umar Dan Sulaika da sauran manya manyan hakimai da dagatai da masu unguwanni

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *