An koma da Danbalki kwamanda Zuwa gidan Kurkuku Sakamakon Alƙalin da ke shari’ar bashi da lafiya saboda haka ba zai iya sauraren karar ba a yau, Don haka an ɗage shari’ar har zuwa ranar Alhamis mai zuwa.
Gwamnatin kano ce ta gurfanar da Kwamanda a gaban Kotun Sakamakon Zargin kalaman tunzura jama’a domin yin tawaye ga gwamnatin jihar Kano akan lamarin da ya shafi Masarautun jihar kano.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa a makon da ya gabata aka gurfanar da Danbilki Kwamanda a gabon kotun majistiri dake Noma’s Land, inda bayan sauraron karar kotun ta aike da shi gidan yari har zuwa wannan rana domin cigaba da sauraron karar.
Danbilki Kwamanda dai yayi kaurin suna wajen kalubalantar manufofin gwamnatin jihar Kano da kuma jagoran darikar Kwankwasiyya Engr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V