Yadda Take Kasancewa A Shekara 1447 AH 2025/26 Wajen Fitar Da Zakka, Sadaki, Dayyar Rai

IMG 112410 09126 1767954257895

Alfijir Labarai ta jiwo hukumar Shari ah ta jihar Kano ta wallafa yadda nusabin zakka, sadaki da diyyar rai yake ta bana shekarar 1447 Ah 2025/26, kamar yadda ta saba duk shekara.

      MAFI KARANCIN SADAKI

Mafi Karancin Sadaki N143,437:00 amma mutum zai iya bada sama da haka bisa kyautatawarsa.

   Kimar Yanke Hannu A Sata

₦143,437.00 shi ne kimar da za a yanke hannu a idan mutum yayi sata.

Nísabin Zakka zai fara daga N11,475,000:00.

Za a kasa wannan kudin gida (40) wanda zai zamo N286,875:00 shi za a bayar.

Idan kudin ya kai Miliyoyi, Kowacce Miliyan Daya za a fitar da N25,000:00, 4. Kudin Azurfa, Nisabin Zakkarsa zai kama N991,085:55, abin da za a fitar shi ne N24,777:14

Sadaki a azurfa N14,866:28

Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci, sakamakon hawa da saukar Dinare da Azurfa

Diyyar Rai A Musulunci: N571,750,000:00

Wannan kimar nisabin zai iya sauyawa daga lokaci zuwa lokaci,
sakamakon hawa da saukar Dinare da Azurfa.

NISABIN ZAKKAR DABBOBI
RAKUMA

RAKUMA: Daga (5 – 9) Akuya 1

Daga (10 – 14) Awaki 2.

Daga (15 – 19) Awaki 3

Daga (20 – 24) Awaki 4.

Daga (25) abin da yai sama za a fitar daga Rakuma.

SHANU: Daga (30) za a ba da Maraki

AWAKI/TUMAKI: Daga (40-120) za a ba da Akuya/Tunkiya.

Idan suka kai dari da ashirin da daya sai a ba da biyu har Zuwa dari biyu da daya, sai a ba da uku, daga nan kowace dari za a ba da ɗaya.

NISABIN ZAKKAR AMFANIN GONA

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa goma (1/10) na noman ruwan sama, kwano (30).

Abin da ya kai kwano (300) wanda yake daidai da wusiki 5, za a fitar da kashi daya bisa ashirin (1/20) na noman rani, kwano (15).

Wannan shine yadda zata kasance a wannan shekara ta 1445AH

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *