Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume na ganawa da ministoci kan zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da matasan Nijeriya ke shirin yi a fadin kasar nan.
Alfijir labarai ta ruwaito ganawar wadda ministoci sama da 40 suka halarta, na da nufin nemo mafita game da zanga-zangar da ake shirin shiga.
Wasu daga cikin ministocin sun hada da Nyesom Wike (Abuja), Yusuf Tuggar (Alβamuran kasashen waje), Zephaniah Jisalo (Ayyuka na Musamman), Tahir Mamman (Ilimi), da Abubakar Bagudu (Kasafi).
Ragowar su ne Wale Edun (Kudi), Mohammed Idris (Yada Labarai), Bello Matawalle (Karamin Ministan Tsaro), David Umahi (Aiki), da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA) Nuhu Ribadu, da sauransu.
Shugaba Bola Tinubu a ranar Talata ya roki βyan Nijeriya da kada su shinga da zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 1 ga watan Agusta, 2024.
Ya zuwa yanzu dai ba san fuskokin wadanda za su jagoranci zanga-zangar ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai ππ
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj