Yanzu-Yanzu: Allah ya yiwa Dan majalisar wakilai ta Najeriya ya rasu

Screenshot 20231011 102941 com.facebook.katana edit 6352252542257

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Isa-Sabon Birni, a karkashin jam’iyyar APC, Abdulkadir Jelani Danbuga, ya rasu.

Wani mamba mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta Kudu a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Aminu Almustapha (aka Boza) ne ya tabbatar da rasuwar.

A cewar Boza, dan majalisar tarayyar ya rasu ne da misalin karfe 12:30 na daren Talata bayan gajeruwar rashin lafiya.

An ce an kwantar da shi a asibiti da yammacin jiya Talata.

“Za a kai gawar sa zuwa Masallacin kasa domin yi masa suttura, daga nan kuma za a kai gawar Sokoto domin binne shi da misalin karfe 11 na safe,” in ji Almustapha.

Danbuga ya rasu ya bar mata biyu, ‘ya’ya da jikoki da dama.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *