Yari Ya Raba Tirela 240 Na Kayan Abinci Saboda Watan Azum

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Alfijr ta rawaito tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, kuma zabebben Sanata mai wakiltar Zamfara ta Yamma, Honarabul Abdulaziz Yari Abubakar ya kaddamar da rabon Tireloli na kayan abinci guda 240 ga al’ummar jihar saboda azumin watan Ramadan, daga cikin Kayayyakin da aka raba a yau sun hada da Shinkafa da Masara da Gero da Sugar da dai sauransu

Da yake jawabi ga dubban magoya bayan ‘yan jam’iyyar APC a lokacin Gudanar da taron a garin Talatar-Mafara, Abdul’aziz Yari ya ce kowacce karamar Hukuma daga cikin kananan hukumomi 14 za ta samu tirela 10 na kayan.

Ya Kara da cewa, ‘yan gudun hijira Dake fadin jihar za su samu manyan motoci 32, sai kuma marayu zasu Sami Tirela 12, yayin da sukuma kungiyoyi za su samu motoci 10.

Yari ya bayyana cewa, makasudin bayar da wannan kayan a Wannan lokaci shine domin al’ummar jihar su sami sauki musamman marasa galihu don su gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, sai dai ya bukaci wadanda aka damka wa rabon kayayyakin da su ji tsoron Allah su baiwa kungiyoyin adadin buhunan da aka ware musu.

Ya ce “Ina kira ga shugabannin da za su raba kayan da su ji tsoron Allah su baiwa kowa nasa kason” , ya kuma ba da tabbacin cewa zai ci gaba da taimaka wa magoya bayansa da marasa galihu muddin yana da ikon yin hakan.

Yari ya yi kira ga magoya bayan jam’iyyar APC da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda da kuma mutunta doka, ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni a cikin al’umma da su bayar da gudumawa ga mabukata a wannan wata na Ramadan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu aFacebook. Alfijr Labarai YouTube. Best Seller ChannelTwitter. @MusabestsellerInstagram. @musa_bestsellerKo a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *