A Juma’ar nan, 5 ga watan Yuli, 2024, jarumar TikTok, Sayyadda Sadiya Haruna, za ta amarce a karo na bakwai da angonta Babagana Audu Grema a Maiduguri
Alfijir labarai ta ruwaito a ranar Alhamis ne Sadiya Haruna ta dora katin gayyatar daurin auren nata, wanda zai gudana a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.
Auren Sayyada Haruna da angonta mai suna Hon. Babagana Audu Grema na zuwa ne ’yan watanni ƙalilan bayan kotu ta raba aurenta da tsohon mijinta, shahararren dan TikTok, G-Fresh Al-Amin.
Auren Sadiya Haruna da G-Fresh dai bai yi tsawon kwana ba, inda takaddama ta rika dabaibaye zaman nasu, har a karshe suka kare a gana kotun Musulunci.
Dambarwar auren Sadiya Haruna da G-Fresh ta karaɗe kafofin sada zumunta inda ake ta ce-ce-ku-ce a kai, kafin daga karshe kotun ta raba auren.
Mako guda ke nan da Sadiya Haruna ta yi wa G-Fresh wankin babban bargo a lokacin da aka karbi bakuncinta a shirin tattauna na Gabon’s Talk Show, na tauraruwar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon.
Hakazalika a wannan ranar Juma’ar ce kuma za a daura auren tsohuwarjarumar Kannywood, wato Sadiya Gyale a Jihar Kano itama.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj