Za A Yi Kiɗan Ƙwarya Da Shantu Yayin Auren Zawarawa A Kano – Mal Daurawa

Amma ba za mu bar kowa ya shiga da waya ba saboda kada a ɗauki matan mutane suna nishadi,” in ji shugaban na Hisbah

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce za a yi kidan ƙwarya da na shantu domin nishaɗantar da zawarawan da za yi bikinsu a Jihar.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake karin haske a kan shirye-shiryen aurar da zawarawa da ’yan mata 1,800 da gwamnatin Jihar ke kokarin yi.

A cewar Sheikh Daurawa, za a yi shagulgula iri-iri domin nishadantar da ma’auratan, tun da a cewarsa, addinin Musulunci bai hana ba.

Ya ce, “Za mu gayyato masu kidan ƙwarya da na shantu da duk wani nau’i na nishadi da Musulunci ya amince da shi.

“Amma ba za mu bar kowa ya shiga da waya ba saboda kada a ɗauki matan mutane suna nishadi,” in ji shugaban na Hisbah.

Ya kuma ce sun ware wa kowacce daga cikin Ƙananan Hukumomin Jihar 44 Naira dubu 500 domin shagulgulan nishadi a yayin biki.

Gwamnatin Jihar dai ta ware sama da miliyan 800 domin bikin zawarawan.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ba ta sanar da ranar da za a yi bikin ba, amma ta ce tana ci gaba da shirye-shirye.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

One Reply to “Za A Yi Kiɗan Ƙwarya Da Shantu Yayin Auren Zawarawa A Kano – Mal Daurawa”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *