Za’a Karrama Matar Da Ta Tsinci Makudan Kudade A Kasa Mai Tsarki – Amirul Hajji

Daga Shu’aibu Ibrahim Gusau

Amirul hajji na Jihar Zamfara, Alhaji Musa mallaha ya bayyana cewa gwamnatin Jihar Zamfara zata Karrama hajiya A’isha Ibrahim Nahuce wadda ta tsinci makuden Kudi a kasa me tsarki.

Alfijir Labarai ta rawaito Amirul hajji ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake Gusau, ya Kara da cewa Hajiya A’isha Nahuce bisa kyawawan halaye da ta nuna a lokacin aikin hajjin da aka kammala, ya Zama dole a karrama ta.

Mallaha ya ce halin da A’isha ta nuna yana daga cikin nasarorin da hukumar ta samu a aikin hajjin na bana, ya Kara da cewa Hajiya A’isha Nahuce ta zama wadda kasa baki daya zatayi alfari da ita, ta hanyar mayar da kudaden da ta tsinta ta Kuma maidata ga hukumar da ta dace a can kasa mai tsarki wadanda suka kai miliyoyin naira.

Ya kuma bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa ta yi matukar farin ciki da matakin da Hajiya Aisha Nahuce ta dauka, ya Kuma nanata kudurin hukumar na gabatar da Hajiya A’isha Bungudu ga gwamna Dauda Lawal domin yaba mata domin kara karfafa mata gwiwa, Kuma domin sauran mutane su yi koyi da ita ba kawai a kasa mai tsarki ba har ma da ko’ina a duniya.

Alhaji Musa Mallaha ya ce cikin nasarorin da Jihar ta samu shine an kammala jigilar alhazan jihar Zamfara a kan lokaci daga kasa mai tsarki domin duk sun dawo gida, Sai dai ya bayyana nadamarsa na na rasa mahajjaci guda daya daga karamar hukumar Talata Mafara wanda ya rasu a lokacin aikin hajji.

Shugaban ya yabawa kokarin gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal bisa matakan da ya dauka na ganin an kula da alhazan Zamfara yadda ya kamata tare da dabbatar da cewa anyi aikin hajji cikin nasara.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *