
Alfijr ta rawaito Bayan gabatar da takardun shaidar cin zabe da INEC ta gabatar, zababben gwamnan jihar Kano Engr. Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) ya kaddamar da kwamitin sa na mika mulki na 2023.

A wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, babban sakataren yada labarai na zababben gwamnan ya fitar yace, tsohon babban sakataren hukumar kula da manyan makarantu (TETFUND) da NNPP 2023 dan takarar Sanatan Kano ta Arewa Dr. Abdullahi Baffa Bichi ya bayyana a matsayin shugaba na kwamitin mika mulki na Gwamna (GTC), yayin da babban sakataren dindindin, Abdullahi Musa mai ritaya a matsayin sakatare.

Kwamitin rikon kwarya zai gudanar da ayyukan mika mulki cikin tsari daga gwamnatin Ganduje mai barin gado zuwa gwamnatin Abba Gida Gida mai jiran gado.
Mai girma Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado zai kaddamar da kwamitin a ranar Asabar 1 ga Afrilu, 2023 da karfe 2:00 na rana.

A kasa akwai cikakken jerin sunayen manyan kwamatin, yayin da za a bayyana kananan kwamitoci a bangarori daban-daban da kuma kananan hukumomi nan gaba kadan.


Kamar yadda Sanusi Bature Dawakin Tofa babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar H.E. Engr. Abba Kabir Yusuf ya saka hannu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇