Bayan kammala zagayen farko a wasannin da ake bugawa na zakarun nahiyar Turai a ranar Laraba, yau juma’a an fitar da jadawalin gaba.
Hukumar da ke kula da kwallon kafa a nahiyar Turai ta rarraba jadawalin yadda kulob-kulob za su fafata a matakin sili ɗaya ƙwale da zai ba wa waɗanda suka yi nasara damar shiga zagaye na biyu na gasar ta zakarun Turai.
Babban wasan da zai fi jan hankali shi ne wanda za a kara tsakanin Manchester City da kuma Real Madrid.
Manchester City wadda ta lashe gasar Champions League a shekara ta 2023, za ta karɓi baƙuncin Real Madrid a filin Etihad, a ranar 11 ko 12 ga watan Fabarairu sannan bayan mako guda sai ta buga wasa na biyu a Sifaniya.
Ita ma Celtic za ta haɗu ne da Bayern Munich kuma a Scotland za a yi bugun farko kafin a yi bugu na biyu a Allianz Arena na Jamus.
Ga yadda jerin wasannin zai kasance a zagaye na biyu:

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ