Zamu Goyi Bayan Cire Tallafin Man Fetur Baki Daya – Inji – El Rufa I

Gwamnonin Kasar nan Zamu goyi Bayan Zamu Cire Tallafin Man Fetur Baki Daya- Inji – El Rufa I 

Gwamnan jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, Malam Nasir El-Rufai, ya ce a shirye gwamnatocin jihohi suke su goyi bayan gwamnatin tarayya wajen cire tallafin man fetur baki daya.

BBC ta rawaito Jaridar Vanguard ta ambato gwamnan yana bayyana hakan ranar Talata a wajen gabatar da sabbin bayanai na Bankin Duniya reshen Najeriya da aka gudanar a Abuja.

Gwamna El-Rufai, wanda ya yi bayani ta intanet, ya ce idan ba a cire tallafin man baki daya ba, watakila jihohi 35 cikin 36 ba za su iya biyan albashi a shekarar 2022 ba.

El Rufa I ya Kara da cewa, an dade da cire tallafin kalanzir, wanda shi ne ya fi yi wa talakawa amfani ba tare da wata matsala ba, yayin da aka cire tallafi a kan gas wanda manyan motoci suka fi yin amfani da shi .

“Ce-ce-ku-cen da ake yi kan fetur abu ne da a matsayinmu na kasa dole mu tattauna a kansa sanna mu amince kan yadda za a kawo karshensa,” in ji gwamna na jihar Kaduna Mal Nasir El Rufa’i 

Article share tools