Zamu marawa Harris Baya, Bayan Matakin Da Biden Ya Dauka – Ilham Omar.

IMG 20240721 WA0149

Daga Aminu Bala Madobi

Bayan daukar matakin janyewa daga shiga tseren shugabancin kasar Amurka da shugaba Joe Biden yayi, ‘Yan majalisu sun fara mubaya’a ga mataimakiya Kamala Harris.

Ilham Omar ‘yan majalisa ce, tace matakin da Biden ya dauka abune mai kyau, domin baiwa sauran matasa dama su bada tasu gudunmawar.

“A shirye nake domin mubaya’a da bada dukkan goyon bayana ga Kamala Harris a matsayin ‘yar takara daga jamiyyar mu ta
Democrat.

“Inada tabbaci za ta doke Donald Trump a zaben da za a gudanadar a 2025.

Wannan na zuwa ne a gabar da shugaban ƙasar Amurkan Joe Biden, ya bar wa mataimakiyarsa, Kamala Harris, tikitin zama ‘yar takarar shugaban ƙasar Amurka, a jam’iyar Democratic, bayan ya sanarwa da cewa ya hakura da shiga zaben.

Wannan matsaya, da shugaba Biden, ya dauka ta biyo bayan wani matsin lamba da yake fuskanta daga masu ruwa da tsakin jam’iyarsa da suke cewa, shugaba Joe Biden, ya hakura tare da jingine kudirinsa, na sha’awar sake zama dan takarar shugaban Amurka a jam’iyar Democrat.

Rahotanni sun ce Joe Biden, ya gaza kai bantansa, a muhawarar jin manufofin ‘yan takarar shugaban ƙasa Amurka da aka gudanar a ranar 27 ga watan Yuni, tsakanin shugaba Biden, da jam’iyun adawa.

Joe Biden mai shekaru 81 a duniya, zai kammala wa’adin mulkinsa, a ranar 20 ga watan Junairu, 2025.

Ko Kamala Harris, za ta iya kafa tarihin zama mace ta farko a matsayin shugaba a ƙasar Amurka?

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *