Daga Aminu Bala Madobi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin guiwar Hukumar Yaki da Safarar Bil Adama tayi nasarar ceto mutane arbain da takwas daga Ghana zuwa Legas wadanda akayi safararsu.
Alfijir labarai ta ruwaito cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Daraktar wayar da kai ta Ma’aikatar, Hajiya Halima Sani Gadanya ta rabawa manema labarai a yau, ta sanar da cewa aikin ceto karkashin jogorancin kwamishiniyar Ma’aikatar jinkai da magance fatara ta jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi Sani, ta tabbatar da cewa wadanda aka ceto sun hada da mata manya hudu (4) da kananan yara masu shekaru tsakanin 15 da 16 guda ashirin da shida (26) da kuma ‘yan mata goma sha takwas (18).
Kwamishiniyar na duk mai yuwa wajen dawo da wandannan mutane daga Jihar Legas zuwa Kano cikin kwoshin lafiya.
Kwamishiniyar ta samu rakiyar wasu daga cikin daraktocin Ma’aikatar, Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kano da wasu jamian hukumar yaki da safarar bil adama ta kasa.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj