Zanga-zanga: Ba za mu bari a ƙona mana ƙasa ba —  In ji Rundunar soji

FB IMG 1721915788325

Shelkwatar tsaro ta ƙasa ta gargadi masu shirin yin zanga-zanga a fadin kasar cewa duk da cewa hakkinsu ne na zanga-zangar, amma ba za ta amince da tashin hankali ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mutane na yin gangamin zanga-zangar da za a yi a fadin kasar daga ranar 1 ga Agusta zuwa 10 ga Agusta, 2024.

Masu shirya zanga-zangar, wacce aka yi wa laƙabi da #EndBadGovernace, sun koka kan yadda yunwa da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙaruwa a kasar.

Da ya ke zantawa da manema labarai a Abuja a yau Alhamis, Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya ce sojoji ba za su bari a samu tashin hankali a Najeriya ba.

Ya kara da cewa sojojin sun bankado makarkashiyar da wasu marasa kishin kasa suka shirya domin amfani da zanga-zangar tare da mayar da ita tashin hankali ta hanyar kai wa ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba, da kasuwancin su hari.

Ya buga misali da zanga-zangar da ake yi a Kenya, inda ya kara da cewa har yanzu an rasa yadda za a shawo kan lamarin a ƙasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *