Zargin Juyin Mulki: Hukumomin Tsaro Sun Tsare Sheikh Sani Abdulkadir Zariya Don Cigaba Da Bincike

IMG 173833 19226 1771519121554

Hukumar Leƙen Asiri ta Soji (DIA) ta miƙa Malamin addinin Musulunci, Sheikh Sani Abdulkadir Zariya, hannun Hukumar Farin Kaya (DSS), domin ci gaba da bincike kan zarginsa da hannun a ƙoƙarin yin juyin mulki a Najeriya.

An kama malamin ne saboda zarginsa da hannu wajen yunƙurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.

A baya, wani alƙalin Kotun Tarayya da ke Abuja, ya umarci DIA da ta kawo malamin kotu a ranar 18 ga watan Fabrairu domin duba yiwuwar bayar da belinsa. Hannunsa Ga DSS

Sheikh Abdulkadir ya shigar da kara na hakkin ɗan kasa, yana neman a sako shi nan take, yana ikirarin tsare shi ba bisa doka ba.

Iyalinsa sun bayyana cewa tsare shi na da alaka da wani canja kudi na Naira miliyan 2, wanda ake danganta shi da zargin juyin mulki.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *