Zargin Maita: Wani matashi ya kashe mahaifiyarsa.

IMG 20231213 WA0004

Wani matashi mai suna da Sadiq Idrissu, ya kashe mahaifiyarsa a Jihar Adamawa, kuma ya bayyana cewa bai yi nadamar kisan gillar da ya yi mata ba.

Alfijir labarai ta rawaito matashin mai shekaru 30, ya kashe mahaifiyarsa ne ranar 05 ga watan Disemba 2023, a garin Boga cikin karamar hukumar Gombi a jihar, maimakon nadama kan kisan gillar da yai mata, amma cewa “ban yi nadamar kisan da na yi wa mahaifiyata ba” in ji matashin.

Ya ci gaba da cewa “na kashe ta ne, saboda ta bayyana min ita mayya ce, da ma jama’a na zarginta da maita, kuma gaskiya ne, domin tana aikata wasu abubuwan mamaki, musamman da daddare.

“Mamana tana bayyana min a cikin mafarki a matsayin mayya, tana kuma jefa min tsoron da ke hana ni yin bacci da daddare” in ji matashin.

Al-Manasik Reporters

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *