Zulum Ya Amince Da Bawa Ma’aikatan Rancen Biliyan 2, Da Kuma Kawo Motoci Sufuri 30

Gwamna Babagana ya sanar da ware motocin bas guda 30 da za a sadaukar domin kai ma’aikata guraren ayyukansu.

Alfijir Labarai ta rawaito Gwamna Babagana Umara Zulum, a ranar Talata, ya gabatar da cakin kudi naira biliyan 2 ga kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) reshen jihar Borno don bayar da rancen da babu ruwa ga ma’aikatan da suka cancanta, domin rage radadin cire tallafin man fetur.

Hakan na zuwa ne bayan wata ganawa da gwamnan ya yi da wakilan kungiyar NLC karkashin jagorancin shugabanta na jihar, Kwamared Yusuf Inuwa, a gidan gwamnatin Jihar.

Zulum ya roki kungiyar da ta tattauna da ma’aikatar kudi ta jihar don tantance ma’aikatan da za su samu rancen, da kuma hanyoyin karbar rancen kudin ta hanyar cire akalla kashi daya bisa uku na albashi a duk wata.

Gwamnan ya kuma sanar da ware kashi 100 cikin 100 na kudaden garatuti da ake biya a duk wata.

An kara kudin ne daga Naira miliyan 100 a duk wata, wanda ya kai Naira biliyan 1.2 a duk shekara zuwa Naira miliyan 200 a duk wata, wanda yanzu zai kai Naira biliyan 2.4.

Hakazalika a sakamakon ganawarsa da kungiyar NLC, Gwamna Babagana ya sanar da ware motocin bas guda 30 da za a sadaukar domin kai ma’aikata guraren ayyukansu.

Hukumar Sufuri ta Borno Express ce za ta kula da motocin bas din, amma za a tura su ne manyan tituna don kwashe ma’aikata da safe zuwa sakatariyar Musa Usman sannan a dawo da su da yamma daga sakatariyar zuwa inda aka dauko su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *