Zuwa baɗi rashin tsaro zai zama tarihi a Nijeriya — In Ji Gwamnatin Taraiya

FB IMG 1703138272721

Gwamnatin taraiya ta ce ta fahimci matsalar tsaro da ke addabar kasar nan, ta kuma yi alkawarin kawo karshen ta kafin karshen 2024.

Alfijir labarai ta rawaito Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle ne ya bayyana haka a wata hira da BBC Hausa.

Matawalle ya kara da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace na yaki da ƴan bindiga kafin su kai farmaki, musamman a yankin Arewa mai fama da rikici.

“In Allah ya yarda, daga yanzu zuwa Nuwamba na 2024, za a shawo kan dukkan kalubalen tsaro,” in ji Matawalle.

Ya ce matakan da dabarun da ake dauka za su kawo karshen wannan barazana, inda ya ce matakan sun hada da tunkarar ‘yan bindigar a maɓoyarsu kafin su kai farmaki da murkushe su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *