Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Mai Ta Bukaci FCCPC Ta Binciki Zargin Da Akewa Matatar Dangote.

FB IMG 1770323627794

Wata ƙungiyar ’yan kasuwar man fetur a ɓangaren saye da rarrabawa, ta bukaci Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki ta Kasa (FCCPC) da ta gaggauta bincikar zargin da ake yiwa Matatar Dangote na mamaye kasuwar man fetur ta hanyar amfani da tsarin farashi da ka iya kawo tasgaro da tauye hada hadar cinikayya a kasuwanni.

A cewar ’yan kasuwar, wannan salo da tsarin farashi na matatar yana hana daidaito da adalci a kasuwanci tare da barazana ga dorewar harkokin mai da rashin tabbas a Najeriya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, ƙungiyar ta jaddada cewa an kafa hukumar FCCPC ne domin yaƙi da duk wata barazana dake hana kaushin gasa a kasuwanni tare da tabbatar da adalci a tattalin arzikin Najeriya.

Ehugabannin sun ƙara da cewa, wannan hurumin hukumar ya haɗa da sa ido kan hulɗar kasuwanci tsakanin ’yan kasuwa daban-daban — dillalai, masu sayarwa da sauran mahalarta kasuwa — domin hana ƙoƙarin mamaye kasuwanci da kare masu saye daga cin zarafi.

’Yan kasuwar sun zargi Matatar Dangote da yin wasu ayyuka da ake kallo a matsayin wani gwadabe na tafiyar kasuwancin da ba tare da shigo da kowa tsindim a harkar ba.

Kungiyar ta buga misali cewa wasu lokuta ana sayar da kaya da farashi tabbatacce da kowa ya aminta dashi, amma bayan an kammala saye, sai kamfanin ya sanar da rage farashi ba tare da mayar da banbancin kuɗi ga waɗanda suka riga suka saya ba. Misali, idan aka sayi kaya kan ₦700, daga baya a rage farashin da ₦100 ba tare da maido da kudin da aka rage ba.

Masu ruwa da tsaki na kungiyar sun jaddada cewa manyan masu saye — musamman waɗanda ke sayen miliyoyin lita — su ne suka fi fuskantar wannan matsala. A cewarsu, bayan an loda kaya a farashin da kowa ya amince, Daga baya sai a rage farashi, wanda hakan ke rage sha’awar saye a manyan sikeli tare da haifar da rashin tabbas a kasuwa. Sunce wannan lamari na dakile bunƙasar cigaban kasuwanci.

Sanarwar ta kuma nuna cewa hauhawar farashi da kayyade farashi ba bisa ka’ida babbar barazana ce kuma laifuka ne a ƙarƙashin dokokin Najeriya, Kuma hujumar FCCPC na da ikon ɗaukar matakin doka kan masu laifi.

’Yan kasuwar sun bukaci hukumomin kula da harkokin mai dasu yi aiki kafada da kafada da hukumar FCCPC domin bincike mai zurfi kan duk wani take hakkin farashi.

“Manufar ita ce kawai a binciki duk mai kokarin tada zaune tsaye kan lamarin saita farashi da ke cutar da masu amfani dasu,” in ji ƙungiyar

Ƙungiyar daga bisani ta jaddada cewa damuwarta ita ce a tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin farashi, domin yin biris kan lamarin ka iya dagula lamura

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *