Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Yayin Sallar Juma’a a A Kaduna

FB IMG 1709368775063

Gwamna Uba Sani ya sha alwashin yin bakin ƙoƙarinsa don ganin an kuɓutar da dukkan ɗaliban.

Alfijir labarai ta rawaito wasu ƴan bindiga sun kai hari kan ɗaruruwan Musulmai a yayin da suke sallar Juma’a a wani yanki na Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a arewacin Nijeriya, kamar yadda shugabannin yankin suka bayyana.

Ƴan bindigar sun kai hari ne a unguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari a lokacin da Musulmai ke sallar Juma’a da misalin ƙarfe biyu na rana.

Mazauna ƙauyen da shugabannin al’ummar yankin sun tabbatar da mutuwar mutane tare da jikkatar wasu sakamakon harin.

Wani shugabann al’ummar ƙauyen Malam Muhammad Hudu ya ce an bindigar sun buɗe wuta kan masallatan lamarin da ya tilasta musu tsere a daidai lokacin da suke raka’ar ƙarshe.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Kaduna Mansur Hassan ya tabbatar da kai harin ko da yake bai yi ƙarin bayani kan mutanen da suka mutu ko jikkata ba.

Hakan na faruwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ƴan bindiga sun sace wasu mutane a Angwar Kanawa da ke yakin na Birnin Gwari.

Kazalika lamarin ya faru ne kwana biyu bayan wasu yan bindiga sun sace ɗaliba sama da 280 da malamansu a wata makarantar firamare ta ƙauyen Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chukun.

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ya bai wa jami’an tsaron ƙasar umarni su “gaggauta” kuɓutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihohin Borno da Kaduna da ke arewacin ƙasar.

A ranar Laraba ne wasu ƴan bindigar suka sace gomman mutane, galibinsu mata da ƙananan yara ƴan gudun hijira a Gamboru Ngala yayin da suka je daji domin saro itacen girki.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *