Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da kisan wani kansila a ƙaramar hukumar Funtua da ke jihar Katsina ta arewa maso yammacin Najeriya.
Alfijir Labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin sa’ilin da ƴan bindigar suka kai hari a unguwar Nasarawa da ke a karamar hukumar ta Funtua.
Mai magana da yawun rundunar Ƴan sandan Najeriya a jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce bayanan da suka tattara sun tabbatar da mutuwar kansilan mai suna Samaila Buhari Mairago.
Iyalan mamacin sun ce tuni aka yi jana’izar sa a yau Talata.
Funtua na ɗaya daga cikin yankunan da ke fama da matsalar tsaro ta ƴan fashin daji a jihar ta Katsina.
Kuma yankin na maƙwaftaka da jihar Zamfara, wadda matsalar tsaron ta yi wa ƙamari.
BBC Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb