Jami’an tsaron yan sandan babban birnin tarayya, Abuja sun bazama neman wani ƙasurgumin ɓarawon da yayi awun gaba da mota kirar Hilox, daya daga cikin Motocin mai bawa shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu a masallacin juma’a a birnin tarayya, Abuja.
Lamarin ya faru ne a jiya juma’a da misalin karfe 1 na rana inda aka taru a babban masallacin ‘Abuja Municipal area Council’ (AMAC) dake area 10, Garki Abuja.
Masanin tsaro, Zagazola Makama shima ya bayyana hakan a shafinsa na Manhajar X, inda ya bayyana cewar lamarin ya faru ne a ranar juma’a, inda suka fito daga sallah basu ga Mota ba.
A cewar majiyar, ɓarayin sun sace motar ne da misalin karfe 2 na rana, inda a halin yanzu Gamayyar jami’an tsaron yan sanda suka bazama domin nemo wannan mota kirar Hilox.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD