Wasu yan bindiga sun yi awon-gaba da Sagiru Umar Kofa, jami’in alhazai na ƙaramar hukumar Bebeji a jihar Kano.
Alfijir Labarai ta rawaito ƴan bindiga sun kutsa kai cikin gidan Sagiru da tsakar dare, inda su ka yi wanon gaba da shi.
Sagiru dai shi ne hadimi na musamman ga Abdulmumin Jibrin Kofa, ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Bebeji a Majalisar Wakilai.
Kawo yanzu dai yan bindigar ba su tuntubi iyalan Sagiru din ba.
Ko da mu ka tuntubi kakakin rundunar ƴansanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ba mu samu jin ta bakin rundunar ba sakamakon bai daga wayar da muka kira shi ba, sannan bai bada amsar sakon kar-ta-kwana da mu ka aika masa ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM