Ƴan Sanda Sun Damke Ɗalibin Jami’a Kan Laifin Kashe Budurwarsa Da Wuƙa

Ƴan sanda a jihar Edo sun kama wani dalibi na jami’ar Port Harcourt, UNIPORT mai shekaru 24 bisa zarginsa da daɓa wa budurwarsa wuƙa ta kuma yi ajalinta.

Alfijir Labarai ta rawaito Kwamishinan Ƴan Sandan jihar Edo, Muhammed Ɗan Kwara ya shaida wa manema labarai a jiya Talata a Benin cewa mai gidan hayar wanda ake zargi ne ya kai rahoton kisan ga ƴansanda.

Mai gidan hayar, a cewar Kwamishinan, ya shaida wa ƴan sanda cewa dalibin ya daba wa yarinyar wuka sau da yawa a wuya da kuma a kirji.

Nan take jami’an ƴan sanda su ka garzaya inda lamarin ya faru, suka kuma yi nasarar kama wanda ake zargin, sannan suka kwato wukake guda biyu, inda suka garzaya da matar zuwa asibiti inda aka ajiye gawarta a mutuware.

“Kayan da aka kwato daga hannun wanda ake zargin sun hada da wukake guda biyu masu dauke da jini, wayoyin iPhone guda biyu, wayar Nokia daya, kwamfutar tafi-da-gidanka daya, da kuma katin ATM guda biyu.

“An mayar da lamarin zuwa sashin kisan kai na sashen binciken manyan laifuka na jihar Benin.

Za a gurfanar da wanda ake zargi da laifin kisan kai nan ba da jimawa ba,” in ji Mista Dankwara.

Da ya ke zantawa da manema labarai, wanda ake zargin ya ce marigayiyar ta kawo masa ziyara ne daga Asaba, amma sai ya ga wasu abubuwa kamar na asiri a wajen ta.

Ya ce hakan ne ya haifar da cece-kuce tsakaninsu har ya kai ga yarinyar ta daɓa masa wuka, inda shi ma ya rama daidai da yadda ta yi masa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *