2027: Kwankwaso ya baiyana aniyar sa ta tsayawa takarar shugabancin ƙasa a NNPP

Kwankwaso

Jagoran jam’iyyar (NNPP) na kasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya bayyana kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa a 2027.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN, ya ruwaito tsohon gwamnan na Kano ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP a shirye take ta karbi ragamar shugabancin kasa, jihohi, da sauran mukamai a fadin kasar nan a shekarar 2027.

Kwankwaso, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, ya yi magana ne a yayin kaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP a Katsina ranar Asabar.

Ya je Katsina ne domin ziyarar ta’aziyya ga iyalan ‘Yar’aduwa bisa rasuwar mahaifiyar su, Hajiya Dada.

A cewarsa, jam’iyyar na kan hanyar samun nasara a zaben 2027 mai zuwa.

Shugaban na Kwankwasiyya ya yi kira ga ‘yan Najeriya musamman mata da matasa da kada su bari a yaudare su da taliya ko kudi a zabe mai zuwa.

A yayin da yake kira ga shugabannin jam’iyyar da su rubanya Kokarin su na ganin jam’iyyar ta samu nasara a jihar da ma kasa baki daya, ya yaba musu da sauran masu ruwa da tsaki a jihar kan gyaran sakatariyar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *