SERAP Ta Yiwa Tinubu Barazanar Awa 48 Ya Saka NNPCL Ta Janye Ƙarin Farashin Man Fetur

FB IMG 1721939691541

Ƙungiyar SERAP mai fafutikar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi amfani da ”matsayinsa ya tilasta wa babban kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya gaggauta janye ƙarin farashin man fetur da ƙungiyar ta kira ‘wanda ya saɓa wa doka’.

Alfijir Labarai ta rawaito cewa a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi ta ce ƙarin kuɗin man fetur ɗin ya saɓa wa kundin tsarin mulki tare da dokokin ƙasar game da kare haƙƙin bil-adama.

SERAP ta kuma buƙaci shugaba Tinubu ya ”umarci babban lauyan gwamnatin ƙasar, Lateef Fagbemi, SAN da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa su binciki zarge-zargen cin hanci da almabazzaranci a ake yi wa kamfanin NNPCL.

Ciki har da kuɗin tallafin ƙwatar kai (bailout), na dala miliyan 300 da kamfanin ya karɓa daga gwamnatin tarayya a watan Agustan da ya gabata, da kuma zargin kamfanin da rashin saka ribar mai a asusun gwamnati.

SERAP ta ce “ya kamata a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifi a NNPCL a gaban kotu domin su fuskanci hukunci, idan har an same su da laifi, tare da ƙwato duk abin da suka sata”.

ƙungiyar ta kara da cewa cin hanci da rashawa da ake zargin samu fannin man fetur da kuma kashe kuɗin gwamnati ba bisa ƙai’da ba, da kuma yin ƙunbiya-ƙunbiya ko rufa-rufa sun taimaka wajen ƙarin taɓarɓarewar al’amura a kamfanin, wanda kuma shi ke haifar da ƙarin kuɗin man fetur a koyaushe a ƙasar.

BBC

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *