Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutun Ma aikata Ta Bana

Alfijr ta rawaito Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ne ya bayyana ranar Litinin 1st May a matsayin ranar hutu a madadin gwamnatin tarayya.

Ministan, a wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Shu’aib Belgore a ranar Juma’a, ya yabawa ma’aikatan kan kwazonsu da sadaukarwa, inda ya ce kokarin da suke yi na da nasaba da daukakar kasa da kuma girmama Najeriya.

Ya ce, “Akwai mutunci a cikin aiki, dole ne mu kasance da himma ga aikin da muke yi saboda yana da mahimmanci ga gina kasa.”

Sanarwar ta umurci ma’aikata da su yi koyi da al’adar samar da kayayyaki, tana mai cewa “Karshen aiki shi ne yawan aiki.

Yawan aiki ne ke kaiwa ga samar da kayayyaki da ayyuka masu gamsarwa da samar da wadata.

Don haka ita ce hanyar samun ci gaban kasa da kuma daidaikun mutane.”

Tana kira ga ma’aikata da su daga martabar sana’ar su ta hanyar da gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ke yi na inganta harkar mulki da kuma sa daukacin al’ummar Nijeriya su samu mafi girman moriyar al’umma.

A cewar sanarwar, ministan ya yabawa dukkanin hukumomin tsaro bisa nasarorin da aka samu wajen yaki da masu aikata laifuka a fadin kasar nan, domin ya karfafa musu gwiwa da kada su yi kasa a gwiwa wajen dakile masu laifin a duk lokacin da suka daga kai.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *