
Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da tsawaita dokar ta- bacin da ta sanya a wasu jihohin kasar da suke fama da matsalar hare-haren kungiyoyin masu tayar da kayar ba.
Ta bayyana haka ne bayan taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a ranar Alhamis wanda Shugaba Mohamed Bazoum ya jagoranta.
Jihohin da lamarin ya shafa su ne Diffa, Tawa da Tillaberi.
Dokar za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa ranar 29 ga watan Yuli na 2023.
Gwamnati za ta mika bukatar tsawaita dokar ta-bacin ga majalisar dokoki don neman amincewar ta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ