Alfijr ta rawaito aƙalla mutane 38 aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da kananan yara da mata yayin wani harin ‘yan bindiga a garin Takalafiya da ke karamar hukumar Karu a jihar Nasarawa ta tsakiyar Najeriya.

Yan bindigar wadanda har zuwa yanzu ba a kai ga gano su ba, na ci gaba da kai hare-haren sari ka noke kan daidaikun mutane tun bayan wata takaddama da aka samu tsakanin Makiyaya da Manoma.
Rahotanni sun ce tun farko wani manomi ne a yankin Gwanja da ke makwabtaka da Takalafiya ya kalubalanci wani makiyaya da ya saki dabbobinsa suka yi masa barna a gona.
Yayin takaddamar ne kuma makiyayin ya rasa ransa dalilin da ya sanya rikici tsakanin bangarorin biyu.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa manema labarai cewa tun daga wancan lokaci ne ake ganin harin sari ka noke da ke hadddasa asarar dimbin rayuka wanda ake alakantawa da makiyaya.
Ko a ranar Alhamis din da ta gabata anga yadda makamancin harin ya kashe mutane 4 yayinda a juma’a da ta gabata da asabar din karshen mako ‘yan bindigar suka sake gangami tare da kashe mutanen da yawansu ya kai 38.
Wata majiyar labarai ta bayyana cewa a asabar din da ta gabata al’ummar yankin suka gudanar da jana’izar mutane 38 da ‘yan bindigar suka kashe a kauyuka 2.
RFI Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ