Mai Unguwa Ya Gurfanar Gaban Kuliya Bisa Zargin Zamba Da Cin Amana A Kano

Kotun shari’ar addinin musulinci dake zaman ta a unguwar Kwana Huɗu Kano, ta bayar da belin wani mai unguwa bisa zarginsa da aikata laifukan cin Amana, Zamba da kuma haɗa baki.

Alfijir Labarai ta rawaito Laifukan sun saɓa da sashi na 120, 203 da 206 na kunɗin shari’ar Penal Code Low (SPCL)  

Ana tuhumarsa da haɗa baki da wani mai suna Bello da baya gaban kotun inda suka karɓar wa mai ƙara kuɗi sama da naira dubu ɗari bakwai da zummar za a kawo masa Hijabai na mata.

Sai dai bayan da suka ƙarɓi kuɗin basu kawo Hijaban ba, hakan ne ya sanya aka gurfanar da su a gaban kotun.

Mai gabatar da ƙara Aliyu Abidin Murtala ya karanto wa mai unguwa ƙunshin tuhumar da ake yi masa inda nan ta ke ya musanta zargin.

Kotun ta bayar da umarnin a nemo wanda ake tuhuma na biyu .

Bayan hakanne lauyan dake kare mai unguwar ya roƙi kotun ta bayar da belinsa.

Mai gabatar da ƙara sun yi martani kan roƙon da lauyan wanda ake zargi na farko ya yi.

A karshe dai Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya sanya mai unguwar a hannun beli bisa sharaɗin kawo mutane biyu mazauna jahar Kano , da ajiye kuɗi naira dubu ɗari da saba’in da biyu.

Oddity 24

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijir Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *