Tsohon Ministan Najeriya Ya Rasu Yana Da Shekaru 96

Cif Mobolaji Ajose-Adeogun, ministan babban birnin tarayya Abuja na farko ya rasu yana da shekaru 96.

Alfijir Labarai ta rawaito É—an kasuwan wanda ya taka rawar gani a ci gaban Abuja ya rasu a ranar Asabar, 1 ga Yuli, 2023.

Wani dan gidan Oluremi Ajose-Adeogun ne ya tabbatar da wannan labarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

A cikin sanarwar, Oluremi Ajose-Adeogun ya mika sanarwar iyalan nasu dangane da rasuwar tasa.

Cif Mobolaji Ajose-Adeogun, FCIS, CON, JP, ya kasance abin kauna wanda ya yi Minista a karkashin gwamnatin mulkin soja ta Janar Muritala Mohammed.

A lokacin da yake rike da mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja, ya jagoranci shirin babban birnin tarayya Abuja, inda ya bar babban birnin kasar nan da ba a taba mantawa da shi ba.

A tsawon rayuwarsa, Ajose-Adeogun ya rike mukamai daban-daban.

Ya samu nasarar yin aiki a Kamfanin HaÉ“aka Man Fetur na Shell kuma ya ba da gudummawa sosai a fannin Masana’antu da Gidaje.

Bugu da kari, ya rike mukamin sarkin Ita-Aladan, Obun Eko, Isale Eko, Legas.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *