Ibtila’i! Auren Aisha Aliyu Tsamiya tsohuwar Jarumar Kannywood ya mutu!

📸Aisha Aliyu Tsamiya

AUREN fitacciyar jarumar Kannywood A’isha Aliyu Tsamiya ya daɗe da mutuwa.

Alfijir Labarai ta rawaito mutane sun daɗe su na raɗe-raɗi kan idan auren ya mutu ne saboda irin hotunan da ake ganin ta na sakawa a TikTok masu nuna kamar ita ba matar aure ba ce; yadda ta ke saka sautin waƙoƙin Kannywood, ta na bi ta na rerawa ya haifar da kokwanto game da matsayin auren nata.

Binciken da mujallar Fim ta yi a ‘yan kwanakin nan ya tabbatar da mutuwar auren.

Wata majiya mai tushe ta kurkusa da jarumar ta shaida mana cewa auren ya mutu tun a watanni uku zuwa huɗu da su ka gabata.

Majiyar ta ƙara da cewa mutuwar auren “ba wani abin mamaki ba ne saboda irin yadda su ka daɗe su na kai ruwa rana ita da mijin ta.”

Majiya ta ce: “An daɗe ana zaman doya da manja a tsakanin ta da mijin. Ba a yi ma zaton auren zai kawo lokacin da su ka rabu ɗin ba saboda tun farkon auren matsalar ta fara kuma ta rinƙa ci gaba, wanda hakan ya haifar da wasu matsaloliin daga baya wanda su kaɗai su ka sani, sai dai kuma Allah.”

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Majiyar ta ƙara da cewa: “Babbar matsalar da na sani a game mutuwar auren A’isha Tsamiya da mijin ta ita ce, ta na zargin sa da yin soyayya da wasu matan da ita kuma ta ke ganin hakan ba zai yiwu ba. Hakan ya haifar da rigingimu a tsakanin su lokaci zuwa lokaci har daga ƙarshe dai da matsalolin su ka taru su ka yi yawa, abin ya kai ga rabuwa.”

Fim Magazine

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *