Da Ɗumi Ɗuminsa: Kotun daukaka kara da ke Abuja ta kori gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang.

ALFIJIR 1

A hukuncin da ta yanke a ranar Lahadi, babbar mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu, ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta ba dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress, APC Nentawe Goshwe takardar shaidar cin zabe.

Alfijir Labarai ta rawaito Mai shari’a Williams-Dawodu ya yi watsi da hukuncin kotun da ta tabbatar da zaben gwamna Mutfwang, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai inganta ba.

A cewar kotun, hukuncin da kotun ta yanke na yin watsi da karar da jam’iyyar APC da dan takararta suka shigar a kan cewa ‘yan biyun ba su da ruwa a cikin harkokin jam’iyyar PDP da aka zabi Mutfwang a kai. keta sashe na 177 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 kamar yadda aka gyara da sashe na 134 (C) na dokar zabe.

Kotun ta kuma bayyana cewa sabanin hukuncin da kotun ta yanke na cewa batutuwan da ke kunshe a cikin karar da masu shigar da kara suka shigar, batutuwan da suka shafi gabanin zabe ne, dukkansu dai batutuwa ne na gabanin zabe da kuma na bayan zabe kuma ba za a iya daukar matakin hana su ba.

Domin Kallon Shirin FATAKE Mai Dogon Zango Season 1 Da Kuma CIgaba Da Kallon Season 2, Danna wannan Link din👇

https://youtube.com/@ukentertainmentkano?si=PPtuxJz76OuNP_oI

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *