Majalisar Dattawa Ta Magantu Kan Kisan Gillar Da Aka Yiwa Yan Mauludi A Kaduna

IMG 20231205 WA0018

Daga Aminu Bala Madobi

Majalisar Dattawan Najeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo mutuwar mutane da dama a jihar Kaduna.

Alfijir labarai ta rawaito kawo yanzu an sami adadin mutane sama da 80 dasuka rasa rayukan su sakamakon wannan hari da sojoji suka kai da gangan acewar bisa kuskure ne, yayin da wasu ke kwance a gadon asibiti ana kula da lafiyarsu.

Sanata Lawal Adamu Usman, (Mr La), shine dan majalisar dattawan mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, inda yake lamarin kai wannan hari ba abune da zasu bari ya wuce ba

“Wannan abu ne da ba za mu bari ya wuce ba, za mu sa a bincika a gano dalilin da ya sa ake samun irin wannan iftila’i . Mutane na yin ibadarsu a zo a jefa mu su bam, sai mun binciko abinda ya faru kuma a dauki mataki akan wadanda suka kai harin” in ji shi .

Gomman mutane ake fargabar sun rasa rayukansu bayan harin bam da jirgin saman yakin ya kai wa gungun masu Mauludi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi .

Sai dai duk da cewa yanki ne da ke fama tashin hankali sakamakon hare haren ‘yan bindiga amma majalisar dattawan Najeriya ta danganta alamarin kan gazawar sojojin kasar wajani wajan tattara bayanan sirri kamar yadda sanata Lawal Adamu Usman ya ce:

“Akwai gazawa wajan tattara bayanan sirri saboda ba bu yadda za a yi ka saki harsashi idan baka tabbatar da wurin da za ka kai harin ba ballantana bam. Bam babban abu ne kafin a sake shi dole sai an tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane ne a wurin. Kuma idan har akwai sakaci to zamu tabbatar cewa an kama mutane kuma za’a hukuntansu “, in ji shi.

Tun farko anata bangaren gwamnatin jihar kaduna ta kafa wani kwamitin bincike da aka dorawa alhakin gano yadda lamarin ya faru.

Ita ma majalisar dattawan kasar ta ce za ta kafa kwamitin binciken akan alamarin tare da kai dauki ga mutanen da alamarin ya rutsa da su.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *