Rahoton ya tona yadda Emefiele ya saye bankuna biyu ba tare da ya kashe ko sisi ba
Alfijir labarai ta rawaito an bankado yadda tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya siyi bankunan Union, Keystone da Polaris ta barauniyar hanya. Jim Obazee mai bincike na musamman da shugaba Bola ya nada ne ya tona yadda Emefiele ya mallaki bankin Keystone da bankin Polaris ba tare da biyan ko sisi ba.
Binciken ya bayyana yadda wani na hannun daman tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, marigayi Alhaji Ismaila Isa Funtua da Emefiele suka saye bankuna biyu ba tare da biyan ko sisi ba.
Rahoton da Jim Obazee ya mika wa Shugaba Tinubu a ranar 20 ga Disamba, Emefiele ne ya saye bankunan.
Aminiya ta samu wadannan bayanai ne daga wasu takardu daga majiya mai tushe, amma har yanzu ba a bayyana sakamakon binciken ga jama’a a hukumance ba.
Amma gwamnatin tarayya ta ce za ta kwace bankunan biyu da Emefiele ya saya a kan farashi mai rangwame.
“Mun kammala bincike kan wannan ciniki kuma muna dab da dawo da wadannan bankuna biyu ga gwamnatin tarayya,” in ji rahoton.
An dakatar da Emefiele ne kwanaki kadan bayan hawan Tinubu kan karagar mulki.
Jim kadan da sallamar sa ne jami’an tsaro suka kama shi tare da tsare shi bisa zargin sa da laifin zamba.
Daga bisani shugaban kasan ya umarce su da hukumomin yaki da rashawa su binciki ayyukan CBN a karkashin jaogarcin Emefiele.
A ranar Asabar aka sako Emefiele daga gidan yari bayan ya cika sharuddan beli ciki har da biyan Naira miliyan 300.
Lauyoyinsa sun ki cewa komai game da badakalar sayar da bankunan.
Hakalika mai magana da yawun gwamnati bai amsa bukatarmu ta neman karin bayani ba.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp