Sai dai Soyinka ya ki tantance ayyukan Tinubu a ofis kawo yanzu, inda ya ce tantancewar da zai yi a kan gwamnati mai ci zai zo ne bayan shekara daya a ofis
Alfijir labarai ta rawaito Farfesa Wole Soyinka, ya ziyarci shugaban kasa Bola Tinubu a Legas ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa ya tanadi Wasu tsare tsare guda bakwai don ciyar da Najeriya gaba.
Da yake zantawa da manema labarai bayan ziyarar shugaban kasar, Soyinka ya ce, “Na zo nan ne da ajandar guda bakwai kuma mun tattauna sosai kan wadannan abubuwa.”
Wanda ya lashe kyautar Nobel ya bayyana cewar ya tuna cewa a ziyarar da ya kai wa Tinubu a baya, ya ce kada ya tsaya takarar shugaban kasa, inda ya ce tsohon gwamnan na Legas ya yi watsi da shawararsa.
“Ziyarar farko da na yi ita ce ziyarar abin kunya domin na yi kokarin shawo kan shi kada ya tsaya takara, ina ganin na yi rubutu a kan haka. Na shawarci Atiku da shi kansa da su barwa matasa Kasar. Wannan shine karo na karshe da muka hadu shekaru biyar da suka wuce. Ina kiransa a asirce “olori kunkun” ma’ana mai taurin kai. Ya yi watsi da shawarata kwata-kwata.
“Na zo na gan shi ne domin in ji halin da yake ciki bayan ya yi watsi da shawarata. Ina so in ga yadda lamarin yake shi da matarsa. Na kuma zo yi musu barka da Kirsimeti.
“Ka san mu tsofaffin abokai ne, kuma a matsayinsa na abokina na ce masa ‘kada ka gudu,” in ji shi
Sai dai Soyinka ya ki tantance ayyukan Tinubu a ofis kawo yanzu, inda ya ce tantancewar da ya yi a kan gwamnati mai ci zai zo ne bayan shekara daya a ofis.
A cewarsa, wannan al’adarsa ce da magabata na Tinubu tsawon shekaru.
“Wani abu da ka lura da ni shi ne, galibin shugabannin kasa idan sun zo mulki, nakan bar su su kadai ne kusan shekara ta farko. Na san idan sun shigo, ba sa farawa da komai, sai daga baya sukan fara wani abu.
“Don haka, ina da wannan manufa ta kaina; ko Obasanjo, Buhari, ko Jonathan, za ka lura cewa a cikin shekarar farko da kyar na ce komai.
Wannan ita ce ka’idar da nake bi, amma a karshen shekara guda, ka zo ka sake yi mani irin wannan tambayar,” in ji Soyinka.
Channel
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H47OrRBUPHYEeNqV0vwlQp