Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin Gadar Kofar Dan Agundi duk da cewa kotu ta hana shi amfani da kudin kananan hukumomi
Alfijir labarai ta rawaito ranar Juma a nan ne Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da aikin Gadar Tal’udu a kan biliyan 14.45 da kuma Gadar Dan Agundi wanda za a aiwatar a kan kudi Naira biliyan 15.9 a bisa tsarin hadaka tsakanin kananan hukumomi da matakan gwamnatin jihar.
Gwamna Abba ya bayyana cewa ayyukan biyu za su kawo bunkasar arziki a jihar da kuma rage cunkoson ababen hawa a yankunan da aka sanya gadoji.
Gwamnan ya kaddamar da aikin ne bayan wata Kotun Tarayya ta hana gwamnatin jihar amfani da kudin kananen hukumomi a aikin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇