Wata Sabuwa! Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 5 ga Farouk Lawan

IMG 20240126 121313

Kotun koli ta tabbatar da hukuncin shekaru biyar da aka yankewa tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, bisa samunsa da laifin karbar cin hancin $500,000 daga hannun dan kasuwa Femi Otedola.

Alfijir labarai ta rawaito rahotanni na nuni da cewa an dai yi shari’ar Lawan ne da laifin karbar cin hancin dala 500,000 a lokacin wani bincike da ‘yan majalisa suka yi kan tsarin tallafin man fetur a shekarar 2012.

Lauyan Lawan ya bukaci a soke hukuncin da kotun daukaka kara da ke Abuja ta yanke ranar 24 ga Fabrairu, 2022, inda ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari tare da sallame shi a kan tuhume-tuhume biyu daga cikin ukun da ake tuhumarsa da laifin cin hanci da rashawa da gwamnatin tarayya ta yi masa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

One Reply to “Wata Sabuwa! Kotun Koli ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 5 ga Farouk Lawan”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *