Gwamnan Kano Yayi Martani Kan Kiran Da Ganduje Yayi Musu na Komawa APC A Kwararo

FB IMG 1706268378159

Gwamnatin jihar kano ta ce kawo yanzu babu wanda ya tuntubeta game da shiga jam’iyyar APC ta hanyar da ta dace.

Alfijir labarai ta rawaito Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan ya bayyana cewa wannan kira da shugaban APC ya yi musu a kwararo suka ji shi.

”Mun ji bayyanin cewa ya miko wannan ƙoƙon bara na gwamna ya dawo jam’iyyar APC to amma abin mamaki shi ne, shi Ganduje a matsayinsa na tsohon gwamna da tsohon mataimakin gwamna ya fi kowa sanin hanyar da ake isarwa gwamna mai ci sako idan ana son ya je wurinsa”, in ji Sanusi.

Ya kuma kara cewa gwamna Yusuf ba shi da wata matsaya ta barin jam’iyyarsa ko kin barin jam’iyyarsa.

”Amma maganar da muka ji ya faɗa a kafafen yaɗa labarai na zumunta mu ka ji ta kuma a nan mu ka barta’’

”Ka san ita siyasa ko in ce sauya sheka ta siyasa kamar canza gida ne, ba ka tashi lokaci ɗaya kawai ka dauki jakarka ka fita, ka ce wai ka canja gida.

“Akwai abubuwan da za ka iya yi kafin ka ce ka canja gida saboda don haka mu a wurinmu wannan sako mun ji ne kawai kamar a sama”, in ji shi.

Wannan yunkuri na jam’iyyar APC na zuwa ne bayan umarni da shugaba Tinubu ya bayar, na cewa ɓangarorin biyu su je su sasanta da juna.

Wasu dai na ganin cewa abu ne mai matuƙar wuya waɗannan ɓangarori su iya ajiye rigingimun da ke tsakaninsu su yi aiki tare idan ta tabbata cewa za su haɗe, musamman kan wanda zai zama jagora.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

One Reply to “Gwamnan Kano Yayi Martani Kan Kiran Da Ganduje Yayi Musu na Komawa APC A Kwararo”

  1. Gaskiya ne wannan; amma yi ma gwamna magana ba tare da an tauna ta ba, kamar Kwankwaso haka ya inga yi ma mak girma Ganduje, a sanda ya na mulki; shi ya sa, ba zai yu shi kuma ya risinar da kai ga jam’iyyar adawa ba.
    A ganina Ganduje ya na yi ma gwamna iirin wannan kiran, don ya na tunanin dole gwamna zai biyo su, tun da har su ka bar ma sa kujerar gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *