An Bukaci Tinubu Ya Tumbuke Ministansa Kan Dalili 1

FB IMG 1706435261916

Babban Daraktan hukumar CODE, Hamzat Lawal ya bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki kan Minista Nyesom Wike

Alfijir labarai ta rawaito Hamzat ya ce ya kamata Wike ya dauki nauyin duk abin da ke faruwa ganin shi ne gwamnan Abuja ba na Rivers ba. Hamzat ya bayyana haka ne yayin hira da Legit inda ya ce Wike na hada siyasa da kuma hada mulkin birnin Abuja, don haka ya bukaci Shugaba Tinubu ya dauki mataki idan har ba a samu sauyi ba.

. Ya ce: “Wike ya na dauka har yanzu shi ne gwamnan jihar Rivers, ya kamata ya yanke hukuncin ci gaba da siyasar Rivers ko kula da Abuja. “Ya kamata ya sani shi ne mai mulkin Abuja idan aka samu matsala mulkin Tinubu ne ta samu matsala, don haka ba zai yiwu ba.”

Hakazalika “Wike damuwarsa siyasar Rivers ce wanda ke dauke hankalinsa kan abin da ya kamata ya yi a Abuja.”

Idan ba a manta ba, a ‘yan kwanakin nan an yi ta samun muggan hare-haren ‘yan bindiga a birnin Abuja.

A ‘yan kwanakin nan ‘yan bindigan sun yi garkuwa da wasu ‘yan gida daya da suka hada da mata shida da wani namiji.

Idan zaku Iya tunawa, tsohon Ministan Sadarwa, Isa Pantami ya yi martani kan matsalar rashin tsaro yayin da ta kara kamari.

Pantami ya ce a matsayinsa na tsohon Minista yafi kowa jin kunci ganin yadda matsalar ke karuwa. Wannan na zuwa ne yayin da matsalar ta yi yawa a babban birnin Tarayya Abuja a ‘yan kwanakin nan.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *