Daga Aminu Bala Madobi
An Shiga Yakin Cacar Baki tsakanin Gwamna Una Sani Da taohon mai gidan sa Nasir Ahmad El-Rufai inda ya zargi tsaffin gwamnonin Kaduna da yin watsi da manyan asibitoci 32 na jihar tsawon shekaru 20.
Alfijir labarai ta rawaito Gwamna Uba Sani, ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi bakuncin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC daga kananan hukumomin jihar 23 da suka kai masa gaisuwar Sallah a gidan gwamnati da ke Kaduna.
Gwamnan ya ce lamarin ya sanya mazauna jihar ke tafiya wasu gurare domin kula da lafiyarsu.
Ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar gyarawa da sake ginawa da kuma samar da manyan asibitoci guda shida – biyu a kowace shiyyoyin majalisar dattawa uku na jihar.
“A cikin wata daya da ya gabata, na samu rahoto daga mataimakin gwamna, wanda yana daya daga cikin fitattun kwararrun masana kiwon lafiyar jama’a a Najeriya, cewa manyan asibitocinmu 32 da ke Kaduna kamar yadda muke magana, yawancinsu ba sa aiki.” Sani yace.
“Saboda haka, yawancin marasa lafiya daga Kaduna sai sun yi bulaguro zuwa wasu jihohi makwabta domin kula da lafiyarsu.
“Tabbas ba za mu bar hakan tacigaba da faruwa ba. Shi ya sa muka yanke shawarar gyarawa da sake gina akalla manyan asibitoci guda shida daga cikin manyan asibitoci 32. Za a fara wannan aiki da yardar Allah ranar Litinin, wato nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
“Dole ne mu maida hankali a fannin kiwon lafiya saboda galibin wadannan asibitocin da na ambata ba a basu kulawa ba a cikin shekaru 20 da suka gabata, kuma shi ya sa suke cikin halin da suke ciki yanzu.”
Ya kuma ce gwamnatinsa tana mai da hankali kan fannin ilimi.
Ya ce bayan sace yara ‘yan makaranta a yankin Kuriga, gwamnati ta fara tantance duk kananan makarantun sakandare da firamare a jihar.
Sani ya ce akwai sama da makarantu 1,500 da ya kamata a yi musu katanga daidai da tsarin shirin samar da makarantu masu aminci.
“A saboda haka ne na tuntubi wasu mutane masu kishin jihar nan, musamman masu zaman kansu da kuma yadda muke magana, wasu fitattun ‘yan kasar mu a nan Kaduna, wato Kashim Bukar, mai Barbados, da kuma Adamu Atta mai Fifth Chucker, ya yanke shawarar gina mana katangar makarantu 100.
Muna gode musu bisa kokarinsu da goyon bayansu,” inji Uba sani.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk