Inda Ba Kasa! Wasu Kamfanonin A Kannywood Sun Maka Hukumar Tace Fina-Finai A Gaban Kuliya

IMG 20180605 130113 099

Kamfanonin Amart Entertainment da kannywood Enterprises LTD da Hajiya Aisha Tijjani sun Maka hukumar tace Fina-Finai da jihar kano da shugaban hukumar Abba El-Mustapha a gaban kotu bisa dakatar da kamfanonin da hukumar ta yi a kwanakin baya.

Alfijir labarai ta rawaito kamfanonin sun yi karar El-Mustapha da hukumarsa a gaban babbar kotun jihar kano, Inda suka Mika wasu bukatu guda biyu a gaban kotun kuma kotun ta amince musu.

Bukatun dai sune :

1. Sun roki kotun da ta dakatar da duk wani matakin da hukumar tace Fina-Finai da shugaban ta suna dauka akan su har sai an kammala sauraron Shari’ar, kuma kotun ta amince da bukatar.

Kotun ta kuma bukaci hukumar da ta dakatar da dakatarwar da ta yi musu har sai an kammala sauraron karar da masu kara suka shigar.

2. Kotun ta umarci hukumar tace Fina-Finai da shugaban ta da kada su sake su sake shiga al’amuran da suka shafi ayyukan masu kara ko ta wacce fuska.

Kuma kotun ta ce masu karar suna da damar yin duk harkokin su Wanda basu Karya doka ba, don haka a basu damar yin ayyukansu.

Kotun dai ta ce zata Fara sauraren karar a ranar 29 ga watan afirilu shekara ta 2024.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *