Hakan na faruwa ne bayan babban farashinsa ya koma N1,000 makonni biyu da suka Gabata.
A wata sanarwa na cewar abokan cinikin dake siyan lita miliyan biyar ko sama da haka daga matatar za su ci gajiyar canjin farashin N940, yayin da masu sayen lita miliyan ɗaya ko sama da haka za su cancanci farashin N970.
Alfijir Labarai ta rawaito Mista Anthony Chiejina, shugaban sashen sadarwa, ya yi magana game da sabon farashin, Yana mai cewa ya yi dai-dai da manufar kamfanin na sassauta kalubalen tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta.
“Zan iya tabbatar muku da cewa matatar mai ta Dangote ta shiga dabarun hadin gwiwa da gidajen mai da iskar gas na MRS, domin tabbatar da cewa masu amfani da man sun samu siyan mai a farashi mai sauki, a dukkan tashoshinsu na Legas ko Maiduguri.
Kuna iya siyan dizal mai ƙasa da lita 1 akan Naira 1,050 da kuma man jiragen sama akan N980 a duk manyan filayen jirgin da MRS ke aiki.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk
Masha ALLAH