Hukumar yaƙi da cin-hanci ta Kano ta bankaɗo badaƙalar ɗaukar aiki a wasu ma’aikatu

Screenshot 20240613 111941 Facebook

Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarorin dindindin guda uku domin amsa tambayoyi kan badakalar sayar da fom din aiki a ofishin shugaban ma’aikata.

Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Kano a jiya Laraba cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a badakalar.

Ya ce, tuni dubban masu neman aiki damfarar ta shafa.

“Bincike na farko ya gano ayyukan damfara a ofishin shugaban ma’aikata, hukumar ma’aikata, hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano, da hukumar kula da harkokin kiwon lafiya.

“Mutane biyun da ake zargin da ake tsare da su suna bayar da hadin kai ga binciken, wanda ya kai ga rufe shafin ɗaukar aikin na bogi.

“Hukumar tana kokarin kawar da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da an yi adalci a badakalar neman aikin yi da ta damfari dubban masu neman aiki,” in ji Rimin-Gado.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *