Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka yayin taron masu ruwa da tsaki domin lalubo hanyoyin da za’a maganance matsalolin da al’umar jihar Kano ke fuskanta.
Alfijir labarai ta ruwaito Gwamna wanda ya ce za’a samar da hukumar ne domin samar da daidaito Kan farashin kayan masarufi, ya ce samar da hukumar zai taimaka wajen rage halin matsin rayuwa da al’uma ke ciki.
Kazalika ya ce gwamnatinsa ta dawo da tsarin nan na samar da akwatinan da al’uma za su yi amfani dasu wajen isar da sakon shawarwarinsu ga gwamnati kan al’amuran da suka shafi cigaban al’uma da kuma nusar da ita a bangarenda ake da bukatar gyara.
Ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana damuwarsa bisa yadda wasu jami’an tsaro a jihar nan suka tsunduma cikin siyaya tare da bijirewa Umarninsa duk kuwa da cewa shi ne babban jami’in tsaro na farko a jiharsa..
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj