Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Major Mai Ritaya A Kwamishina Tare Da Shugabanin Majalisun Jami’ar Aliko Dangote Da Yusuf Maitama

FB IMG 1723874916966

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya rantsar da Major General Muhammad Inuwa Idris mai ritaya a matsayin sabon kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyuka na musamman.

Alfijir labarai ta ruwaito da yake rantsar da sabon kwamishinan, gwamna Yusuf ya hore shi da ya jajirce wajen sauke nauyin da aka dora masa.

Gwamna Abba Kabir wanda ya taya sabon kwamishinan murna bisa mukamin da ya samu ya ce, zabin nasa an yi shi ne bisa cancanta da kyakkyawan zaton ya zamo mai gaskiya da rikon amna a yayin gudunar da ayyukansa, domin tabbatar da kykkyawan zaton da aka yi masa.

Gwamnan ya ce sabon kwamishinan zai rike sabuwar ma’aikatar tsaron cikin gida da ayyukan na musamman.

A wani ci gaban kuma gwamna Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da shugabannin majalisaun gudanarwar jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote dake Wudil dana jam’iar Yusuf mai tama sule da kuma  na kwalejin fasaha ta jihar Kano.

Da yake kaddamar da shugabannin majalisun manyan makarantun a gidan gwamnati Gwamna Abba Kabir Yusuf yace an zabo wakilan kwamitin ne bisa la’akari da gudummawar da suke bawa cigaban ilimi a jihar kano.

Shugabannin majalisaun gudanarwar manyan makarantun sun hada Mai Shari’a Yusuf Aboki wanda zai jagoranci majalisar gudanarwar Jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote dake Wudil sai tshon mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abubakar a matsayin shugaban majalisar gudanarwar jam’iar Yusuf Maitama Sule da kuma Alh. Buba Galadima, a matsayin shugaban gudanarwar zartaswar kwalejin fasaha ta jihar Kano.

RK

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *