Jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) sun kama shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) Joe Ajaero.
Alfijir Labarai ta rahotanni sun baiyana cewa an kama Ajaero da safiyar yau Litinin a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Ajaero na shirin shiga jirgi zuwa kasar Ingila domin gudanar da wani aiki a hukumance sai DSS ta dauke shi.
Kamar yadda majiyoyi suka bayyana, an bukaci Ajaero da ya halarci taron kungiyar ‘yan kasuwa (TUC) da za a yi a kasar Ingila ranar Litinin.
Sai dai ba a bayyana cikakken bayani da dalilin kama shi ba, majiya mai tushe ta ce an mika Ajaero ga hukumar leken asiri ta kasa NIA.
Daily Nigerian
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj