Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a fadar shugaban Najeriya dake Abuja.
Alfijir Labarai ta rawaito shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da naira biliyan 108 ga jihohin Najeriya 36 domin su shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da sauran nau’ukan bala’o’i.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a fadar shugaban Najeriya dake Abuja.
Da yake karbar bakuncin Kakakin Majalisar Wakilan Kasar, Abbas Tajudeen, mataimakin shugaban kasar ya bayyana halin da ake ciki a birnin Maiduguri da “iftila’in kasa baki daya”.
“Shugaban kasa ya nuna aniya da jajircewa ta yin hadin gwiwa da jihohi domin shawo kan wadannan matsaloli,” a cewar Kashim Shettima.
“A baya-bayan nan, ya amince da sakin naira biliyan uku-uku ga ilahirin jihohin kasar nan domin shawo kan wasu daga cikin wadannan matsaloli domin kowane sashe ya ji cewa ana tafiya tare.”
A nasa bangaren, Abbas Tajuddeen ya jajantawa Shettima da Tinubu da gwamnati da al’ummar jihar Borno, inda ya bada tabbacin cewa majalisun tarayya zasu samar da tallafi ga al’ummomin da ambaliyar ta shafa.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj