Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sarkin Ingila, Charles A Fadarsa

Tinubu

Sarki Charles na Ingila ya karɓi baƙuncin shugaban ƙasa Bola Tinubu a fadar Buckingham dake ƙasar Birtaniya.

Alfijir Labarai ta rawaito Olusegun Dada, hadimin shugaban ƙasa kan sabbin kafafen yada labarai ne ya wallafa hotunan shuagabannin biyu suna gaisawa a shafin X a ranar Alhamis.

Hadimin ya ce an tattauna kan ci gaba da ƙulla alaƙa tsakanin Najeriya da Burtaniya.

“Shugaban ƙasa Tinubu ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Ingila, King Charles a fadar Buckingham”, inji shi.

Shugabannin biyu dai sun haɗu a watan Nuwamba na 2023 kafin fara taron majalisar ɗinkin duniya.

Tinubu dai ya wuce zuwa London ne bayan ziyarar da ya kai ƙasar China.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *